An soke sakamakon zaɓe a Malawi | Labarai | DW | 24.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soke sakamakon zaɓe a Malawi

Shugabar ƙasar Malawi joyce Banda ta ba da sanarwa soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 20 ga wannan wata.

Shugabar wacce ta bayyana haka ta gidan rediyo da telbijan na ƙasar, jum kaɗan bayan sanarwar da hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana. Masu aiko da rahotanin sun ce shugabar ta ɗau wannan mataki ne, bayan bayyana sakamakon, wanda ke nuna cewar ɗan takarar jam'iyyar adawa Peter Mutarika na gabanta da rata mai nisa a cikin sama da kishi 30 cikin ɗari na sakamakon da aka bayyana.

Peter Mutarika dai ƙane ne ga tsohon shugaban ƙasar na Malawi Bingu Wa Mutarika wanda ya yi mulki daga shekaru 2004 zuwa 2012.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba