1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soke izinin ziyarar Ban Ki Moon a Korea ta Arewa

BoukariMay 20, 2015

Hukumomin Korea ta Arewa, sun sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya matakin da suka dauka na soke izinin da suka bashi na ziyarar da zai kai a kasarsu.

https://p.dw.com/p/1FSyN
Kim Jong Un
Kim Jong UnHoto: Reuters/KCNA

Wannan mataki dai ya biyo bayan wasu kalaman da Ban Ki Moon din ya yi, inda ya yi kira ga hukumomin na Korea ta Arewa da su kauracewa duk wani yanayi da zai kara tadda jijiyoyin wuya na fannin soja a yankin tsibirin kasar. Yayin da ya ke halartar wani babban zaman taro a kasar Korea ta Kudu ne, Ban Ki Moon din da kansa ya sanar cewa, da sanyin safiyar wannan Laraba ce ofishin diflomasiyyar kasar ta Korea ta Arewa ya sanar da shi cewa sun soke izinin da suka bashi na kai ziyara a kasar, ziyarar da ita ce irinta ta farko ta wani Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a wannan kasa tun shekaru 20 da suka gabata. Daga nashi bengare ofishin ministan da ke kula da harkokin kasashen na Korea da ke Korea da Kudu ya ce shi ma bai ji dadin wannan lamari ba.

 

 

 

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu