1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya zo gaban goshi a Kwango

Schwikowski Martina MNA
December 19, 2018

A karshen watan nan na Disamba wato 23 ga watan za a gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Sai dai fargaba na karuwa a kasar.

https://p.dw.com/p/3AO6n
Feuer zerstört Wahlgeräte in Kinshasa
Hoto: AFP/Getty Images/J. Wessels

Kwanaki kalilan gabanin a gudanar da zaben shugaban kasa a Kwango an shiga hali rashin sanin tabbas a kasar. Wata gobara da ta tashi a wani wurin ajiye kaya na hukumar zaben kasa ta CENI, ta lalata na'aurorin zabe akalla dubu takwas da aka so yin amfani da su karon farko a Kinshasa babban birnin kasa. A hira da tashar DW Shugaban hukumar zaben Corneille Nangaa ya bayyana gobarar da babban koma baya ga zaben da ake shirin gudanarwa a ranar 23 ga watan nan na Disamba. Shugaba Kabila wanda tun bayan rasuwar mahaifinsa Lauren Desire Kabila a 2001, yake mulkin kasar, a hukumance 2016 wa'adin shugabancinsa ya kare tun a 2016, ya yi ta jan kafa a kan ya sauka. An yi ta fama da zanga-zanga da a wasu loktuan dakarun tsaro ke murkuse su da bakin bindiga. Daga baya shugaban ya ja gefe guda yana kuma fata dan takara da ya nada wato Emmanuel Ramazani Shadary da ke zama tsohon ministan cikin gida, ya ci zaben. Ana kuma kyautata hakarsa za ta cimma ruwa kasancewa 'yan adawa sun yi rauni saboda rashin hadin kai a cewar Gesine Ames ta hadaddiyar kungiyar majami'un yankin Tsakiyar Afirka.

DR Kongo Wahlkampf Martin Fayulu
Hoto: Reuters/S. Mambo

A tsakiyar watan Nuwamba manyan jam'iyyun adawa bakwai sun amince da tsayar da dan takara guda wato Martin Fayulu, amma daga baya wasu jam'iyyun sun janye amincewarsu. Jagororin 'yan adawa Jean Pierre Bemba da Moise Katumbi da aka hana su tsayawa takata, suna goya wa Fayulu baya. Yayin da daya bangaren na 'yan adawa da a kunshi Felix Tschisekedi da Vital Kamerhe za su takara a hade.