An sha artabu a masallacin Kudus
July 27, 2017Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce an yi taho mu gamar ne daf da shiga masallacin idan masu ibadar suka taru bayan sallah suna murnar kafin 'yan sanda Israi'la su far musu, su kuma su mayar da martani da jiffa da duwarwatsu da kwalabe. tun da farko Hukumomi Falasdinu sun yin kira ga jama'ar kasar da su sake komawa a yau Alhamis don yin sallah a mallacin na birnin Kudus.