Sauyi a shugabancin tsaron Jamhuriyar Nijar
January 13, 2020Talla
Labari da dumi-duminsa na cewa gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta maye gurbin mayan hafsoshin sojojin kasar biyu bayan harin da ya halaka kimanin sojoji 89. An karanta sanarwar a gidan rediyon gwamnati.
An nada Janar Salifou Modi babban hafsan tsaro sannan Birgediya-Janar Seidou Bague a masayin babban hafsan sojan kasa inda ya maye gurbin Sidikou Issa. Shugaba Mahamadou Issoufou ya amince da matakin yayin taron majalisar zartaswa ta kasar gabanin tafiya taro a kasar Faransa.