1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudi na maraba da 'yan bude ido

Zainab Mohammed Abubakar MAB
September 28, 2019

Saudi Arabiya ta bude kofofinta ga masu yawon bude ido na ketare inda ta kaddamar da sabbin damarmaki na samun izinin shiga kasar ga kasashe 49 na Turai da Asiya da Amirka

https://p.dw.com/p/3QOIl
Saudi-Arabien König Salman
Hoto: Getty Images/AFP/A. Caballero-Reynolds

Mahukuntan na Riyadh dai na ganin cewar wannan bangaren zai bayar da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikinta da wajen kashi 10 nan da shekarata 2030 bayan bayar da dama ga baki 'yan yawon bude ido. A shekarun baya bayannan dai masarautar ta Saudiyyar na ci gaba da sassauta matsayinta musanmman a fannonin rayuwar al'ummarta.

A yanzu haka dai 'yan asalin kasashen Amirka da Rasha da China da Japan da wasu kasashen nahiyar Turai na iya samun izinin shiga kasar ta yanar gizo ko kuma da zarar sun isa kasar, akan kudi dalar Amurka 120. Kana mutum na iya zama na tsawon watanni uku a cikin kasar.