1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar taron shata sabuwar ƙasar Yamen

Usman ShehuFebruary 6, 2013

Shugaban ƙasar Yamen ya sanar da ranar gudanar da babban taron sasantawa don inganta demokradiyar kasar

https://p.dw.com/p/17ZtC
Yemeni Army soldiers stand in line during the visit of Interior Minister Abdelqader Qahtan and Defence Minister General Mohammed Nasser Ahmed at a military base in the restive southern province of Abyan on July 2, 2012. Yemeni troops recaptured a string of Al-Qaeda bastions across the troubled south and east last month, where the militants had seized control last year. AFP PHOTO/STR (Photo credit should read -/AFP/GettyImages)
Sojojin kasar YemenHoto: AFP/GettyImages

Shugaban ƙasar Yamen Abdurbuh Mansu Hadi, ya sanar da ranar 18 ga watan gobe, a matsayin ranar da za a gudanar da taron sasanta al'ummar ƙasar, wanda aka daɗi ana zumuɗin fara shi. Hadi ya kwatanta taron a matsayin babban ginshiƙi wajen makomar ƙasar da ke ci gaba da yin kwaskwarima bisa kafofin gwamnati, bayan kawar da shugaban kama karya Ali Abdallah Saleh da yan ƙasar suka yi. Taron ana saran zai shirya sabon kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe wanda zai gudana baɗi idan Allah ya kaimu, ana saran zai kasance mai tarihi a siyasar ƙasar Yamen. An dai zabi Abdurbuh Mansur Hadi a matsayin shugaban riƙo, bayan kawar da shugaba Saleh da ya yi shekaru 33 yana mulkin ƙasar. Don haka shugaban ya buƙaci dukkan yan siyasa da su halarci taron da zai shata wata sabuwar ƙasar Yamen.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu