An samu tsohon mataimakin shugaban Kongo da laifi | Labarai | DW | 21.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu tsohon mataimakin shugaban Kongo da laifi

Kotun manyan laifukan yaki ta duniya ta samu Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo da laifi.

Kotun hukuntan manyan laifukan yaki ta duniya ta samu Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo da laifin ta'asa na yaki da dakarunsa na-sa-kai suka aikata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Alkalan kotun sun samu Bemba da duk laifuka biyar da aka tuhume shi wadanda mayakan sa-kai da ke karkashin ikonsa suka aiwatar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Shi dai Jean-Pierre Bemba tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo ya zama wani babban jigo da kotun ta samu da laifi.