An samu Pistorius da laifin kisa ba da gangan ba | Labarai | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu Pistorius da laifin kisa ba da gangan ba

Kotu a Afirka ta Kudu ta ce ta samu dan tseren nan da ya samu lambobin yabo iri-iri wato Oscar Pistorious da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp amma ba da nufi ba.

Mai shari'a Thokozile Masipa ce ta bayyana hakan bayan da ta kammala yanke hukunci a zaman kotun na safiyar wannan Juma'ar.

Mai shariar ta kuma ce kotun ta same shi da laifi na amfani da bindiga ba bisa ka'ida ba amma kuma an wanke shi daga sauran zarge-zargen kan mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Ranar 13 ga watan gobe ne dai ake sa ran kotun za bayyana irin daurin da za ta yi wa Mr. Pistorius kan laifin kisan kai ba da gangan ba da kuma batun na amfani da makami ba bisa ka'ida ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman