An samu koma baya a matsalar cin hanci a 2016 | Siyasa | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An samu koma baya a matsalar cin hanci a 2016

Kungiyar da ke kula da yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International ta bayyana rahotonta a kan yadda tafiyar ayyukan cin hanci yake a duniya a shekara ta 2016.

Batutuwa biyu ne dai suka dauki hankali a rahoton kungiyar da suka hada da yadda a kasashe da dama aka samu ja da bayan wannan matsala ta cin hanci, da kuma yadda ake ganin wasu manyan kasashe na furta kalaman yaki da cin hanci amma ba tare da cika wa ba. Kungiyar da ke fafutuka wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa a duniya, ta ce idan aka yi la'akari za a ga cewa wannan matsala dai ta dan ja baya idan aka kwatanta ta da ta shekarar da ta gabata, kuma hakan abun a yaba ne amma kuma an gano cewa gwamnatoci na ambaton wannan batu ne na yaki da cin hanci domin sun san cewa batu ne da jama'a da ma bankunan kasashensu ke son ji kamar yanda Finn Heinrich Daraktan da ke kula da fannin bincike na kungiyar ta Transparency International ya ke cewa:

"Gwamnatoci suna yin haka ne a matsayin wani salo na birge jama'arsu, da kuma birge sauran masu son zuba jari a cikin kasashensu. Amma akasarinsu suna magana ne ba tare da cikawa ba.

Infografik Korruptions-Index 2016 ***SPERRFRIST 25.1.2017 05:00 UHR*** POR

Taswirar bayanai na 2016

Kungiyar dai na dogaro ne da bayannai irin na Bankin Duniya ko Asusun ba da Lamuni na Duniya, sannan rahoton na mayar da hankali ne kan yadda ake samun alakar da ke tsakanin cin hanci da rashawa idan ta yi yawa a cikin kasa, da kuma bambancin da ake samu na jin dadin rayuwa tsakanin 'yan kasa kamar yadda Finn Heinrich ya yi tsokaci:

Ya ce: "Ni a ganina a matsayina na mai bincike, alaka tsakanin cinhanci da rashin dai-daito da ake samu tsakanin al'umma batu ne mai bada mamaki. Domin duka fannin biyu na tafiya ne tare, wanda hakan ke haifar da wani yanayi da ke bai wa cin hanci gindin zama tsakanin al'umma da kuma rashin tafiyar da shari'a."

Finn Heinrich da Edda Müller na Transparency

Finn Heinrich da Edda Müller na Transparency

Masanin dai ya gano wasu matakai guda biyu na yaki da cin hanci. Matakan kuwa su ne bi sau da kafa na al'umma tare da sa'ido ga dukkanin abubuwan da ke faruwa a kasarsu, da kuma 'yancin fadar albarkacin baki na kafofin yada labarai. A nan Jamus a cikin jihar Schleswig-Holstein sa'idon da al'umma ke yi kan harkokin jihar ya nuna yadda wannan mataki ke da babban amfani wajen yaki da cin hanci kaman yadda Hans-Werner Rogge na wata kungiya da ke yaki da cin hanci ya yi tsokaci, inda ya ce a shekarar da ta gabata an gabatar masa da batutuwa na cin hanci har guda 64 wanda ba wai wadanda abun ya shafa kai tsaye ne suka bayyana ba al'umma ce ta gani da idonta yadda abubuwan ke gudana kana ta sanar.

Cin hanci dai na janyo babbar asara maras misali ga kasashen da wannan mugunyar akida ke gudana. Kuma ana ganin sakamakon hakan karara a kasashen Afirka, ba su kadai ba ma har da kasashen Turai da Asiya batun cin hanci ya zama ruwan dare.

Sauti da bidiyo akan labarin