Matasa sun ki amsa kiran hukumar zaben Tunisiya
September 15, 2019Talla
Gabannin zaben dai al'ummar kasar sun bukaci sabon shugabancin da za a samu ya magance matsalar karyewar tattalin arziki da kuma rashin aiki tsakanin matasa. Kafin wannan lokaci dai da dama daga cikin al'ummar kasar na yi wa Nabil Karoui guda daga cikin attajiran kasar kyakkyawan zaton zai fitar musu da kitse daga wuta duk kuwa da cewar gwamnati ta zarge shi da musayar kudade ba bisa ka'ida ba.