1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu cikas kan yaki da cutar Ebola

April 5, 2014

An kai hari kan jaim'an kiwon lafiya da ke neman kawar da kwayoyin cutar Ebola a kasar Guinea inda kawo yanzu cutar ta hallaka kimanin 90.

https://p.dw.com/p/1BceC
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Mahukuntan kasar Guinea Conakry sun nemi kwantar da hankali a wannan Asabar bayan gungun wasu mutane sun kai hari kan tawagar jami'an kiwon lafiya da ke neman magance cutar Ebola da ta bulla kasar, sannan ta yi sanadiyar hallaka kusan mutane 90.

Farmakin ya tilasta wa kungiyar likitoci na gari na kowa, medicins sans frontiere, ta jingine aiki a yankin kudu maso gabashin kasar a wannan Jumma'a da ta gabata, bayan hari kan daya daga cibiyoyinta. Lamarin ya faru bisa jita-jitar da ake yadawa cewa jami'an kiwon lafiyar ne suka kawo cutar cikin kasar ta Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka. Amma hukumomin sun ce aikin kungiyar ta likitoci na gari na kowa da sauran kungiyoyin kasashen duniya ya taimaka gaya wajen kashe kaifin yaduwar cutar ta Ebola a kasar.

Kimanin mutane 137 suka kamu da cutar, kuma rahotanni sun ce tuni cutar ta Ebola ta shiga kasashen Mali, da Liberiya da kuma Saliyo, yayin da kasar Senegal ta rufe kan iyakarta da kasar ta Guinea Conakry.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal