1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu barkewar cutar Ebola a Gini

March 23, 2014

Cutar zazzabin Ebola ta hallaka mutane 60 a kasar Gini da ke yankin yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/1BUTp
Hoto: AFP/Getty Images

Jami'an kiwon lafiya a kasar Gini Conakry da ke yankin yammacin Afirka sun tabbatar da mutuwar mutane 60 sakamakaon barkewar cutar zazzabin Ebola, tun farkon wannan Febrairu, sannan ake kyautata zaton wasu mutane 80 yanzu haka suna fama da chutar.

Wannan ya zama karo na farko da aka samu labarin barkewar cutar ta zazzabin Ebola mai saurin kisa cikin kasashen yammacin Afirka, kuma ana damuwa na yuwuwar chutar ta yadu zuwa kasar Saliyo mai makwabtaka da kasar ta Guinea.

Tuni kungiyar likitoci na gari na kowa, Medecins Sans Frontieres, ta tura karin jami'ai da kayan aikin zuwa wuraren da aka samu barkewar cutar ta Ebola, a kasar ta Gini Conakry, domin taimakawa wajen magance matsalar. Masana daga kasar Faransa suka gudanar da binciken da ya tabbatar da cewa cutar Ebola ce ta barke.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar