An samu Bajamushe da kwayoyi a Indonesiya | Labarai | DW | 22.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu Bajamushe da kwayoyi a Indonesiya

Jami'an Indonesiya sun samu wani Bajamushe da gram bakwai na Heroin lokacin da ya isa kasar, lamarin da bisa ga doka ke barazana ga ransa saboda zai iya fuskantar hukuncin kisa bisa laifin safarar miyagun kwayoyi.

Wani Bajamushe mai shekaru 56 da haihuwa na fuskantar barazanar hukuncin kisa a Indonesiya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi. Kamfanin dillancin labaran kasar Antara ya jiyo daga bakin jami'an Kwastam cewa, an kamashi ne a watan Janairu a lokacin da ya isa filin jiragen saman kasa da kasa na Bali dauke da gram bakwai na Heroin. Bisa ga dokar Indonesiya duk mutumin da yake dauke da fiye da gram biyar na miyagun kwayoyi na iya fuskantar hukuncin kisa.

A wani taron manema labarai, an gabatar da Bajamushen ga jama'a tare da wani dan Birtaniya daya da aka tsare bayan a cikin kayansa, ma'aikata suka sami kwayoyin Valium da dama. A cewar hukumomin Indonesiya dan Bittaniyan mai shekaru 48 zai iya fuskantar daurin shekaru goma a gidan yari ko kuma a ci shi tarar kudin da ya kai Euro dubu 17.

Indonesia na daya daga cikin kasashe duniya da ke da tsauraran dokoki kan miyagun kwayoyi, inda a cikin 'yan shekarun nan, aka kashe mutane baan da aka samu da laifin saye ko sayarwa ko shan miyagun kwayoyi.