An sallamo Fafaroma daga asibiti | Labarai | DW | 01.04.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallamo Fafaroma daga asibiti

Kamfanin dillancin labarun Jamus, DPA, ya ce Fafaroman ya gana da 'yan jarida a kofar asibitin da ya kwanta na kwanaki uku, inda ya shaida musu cewa yana nan a raye.

An sallamo shugaban Kiristocin duniya mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis daga asibiti bayan jinyar ciwo mai nasaba da numfashi.

A yayin tattaunawarsa da manema labarai ta wannan Asabar, Fafaroma ya ce zai halarci dandalin Saint Peters Square domin jagorantar taron ibadar da aka saba yi a duk shekara.

Da farko dai mabiya sun nuna damuwa tare da fargabar shugaban na Katolika ba zai samu sukunin jagorantar ibadun Ista da za a yi a wannan wata na Afrilu ba. To amma Fafaroma mai shekaru 86 ya ce tun a ranar Laraba ya fara samun saukin jikinsa, inda ma ya yi amfani da damar wajen jinjina wa malaman asibiti da ya ce sun nuna jarumta wajen samar da waraka.