An sallami Micheal Schumacher daga asibiti | Labarai | DW | 16.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sallami Micheal Schumacher daga asibiti

Likitoci a wani asibiti da ke Grenoble a kasar Faransa sun sallami Micheal Schumacher bayan da ya shafe watanni ya na kwance bayan wani mummunan rauni da ya yi a kansa.

Rahotannin daga Faransa na cewar an sallami dan tseren motocin nan na Formula one na Jamus Micheal Schumacher daga asibitin bayan da ya shafe watanni da dama cikin dogon suma sakamakon wani hadari da ya gamu da shi lokacin da ya ke wasan zamiyar kankara a tsaunukan nan na French Alps da ke Faransa a watan Disambar bara.

Mai magana da yawun Mr. Schumacher din wato Sabine Kehm ta ce yanzu haka an maida shi wani asibiti da ke kasar Switzerland inda nan ne zai cigaba da karbar magani, amma ba ta yi karin haske ba game da irin yanayin da ya ke ciki yanzu haka ba, sai dai wasu rahotanni na cewar ya farfado daga dogon suman da ya yi.

Babu dai wata sanarwa da aka fidda gabannin sallamarsa daga asibitin da ya kwanta a garin Grenoble na kasar ta Faransa amma iyalansa da likitocinsa daga bisani sun mika godiyarsu ga jama'ar kasar da ma na sauran sassan duniya dangane da damuwarsu da suka nuna sakamakon halin da ya tsinci kansa a ciki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe