An sako wasu 'yan jaridu da aka yi garkuwa da su
July 18, 2010Talla
An sako wasu 'yan jaridar Najeriya guda huɗu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin da ake haƙan man fetur na Naija Delta.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito sakataren ƙungiyar 'yan jaridun Najeriya Usman Leman wanda ya tabbatar da sakin 'yan jaridun yana cewar babu wani kuɗin fansa da ƙungiyar ko iyalan 'yan jaridar suka biya kafin a sako sun.
A ranar 11 ga wannan watan ne dai, wasu gungun 'yan bindiga suka sace 'yan jaridun tare kuma da neman diyyar Naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa.
Tuni ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama na ƙasa da ƙasa suka yi kiran a sako 'yan jaridan. Sace mutane domin neman fansa dai abu ne da ya zama ruwan dare a ƙasar ta Najeriya.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Mohammad Nasiru Awal