An sako fursunonin siyasa a Ethiopiya | Siyasa | DW | 18.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An sako fursunonin siyasa a Ethiopiya

A farkon wannan watan ne gwamnatin kasar Ethiopiya ta sanmar da shirin sakin fursinonin siyasa a ci gaba da kokarin ganin dorewar tsarin Demokradiyya a kasar.

Äthiopien Dr Mererra & Medrek (DW/Yohannes G. Egziabher)

Dokta Merera Gudina jagoran 'yan adawa na Ethiopiya wanda aka sallamo daga gidan kurkuku

Gwamnatin Ethiopiya ta saki madugun 'yan adawa na kasar Merera Gudina  a ranar Laraba wanda ya samu tarba daga dubban magoya baya a ci gaba da daukan matakin fara sakin fursunonin siyasar da mahukuntan kasar suka dauki aniya. An dai sallamo madugun 'yan adawar ne daga wani gidan kurkukun da ke wajen birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar tare da wasu manyan 'yan siyasar kasar fiye da 100, kafin da ga bisani a saki wasu fursinonin siyasar su 361 da ga wurare daban-daban a kudancin kasar ta Ethiopiya. Ga kuma abin da ya shaida wa magoya bayansa jim kadan bayan ya shaki iskar 'yanci.

Ya ce : ''Na jima ina fada mu su cewar ci gaba da tsare ni, ba abin da zai taimaka wa gwamnati da shi tun tuni na san jam'iyyarmu da ni, muna kan tsarin doka ne kuma muna tafiyar da al'amuran mu cikin tanade-tanaden da kundin tsarin mulki ya yi mana,mu kuma taka rawa a manyan zabuka hudu da za a  gudanar a kasar nan.''

An dai jima ana zargi kasar Ethiopia da yi wa hakkin 'dan Adam kama karya abin da ya hada da kame wani ko wata kungiya mai adawa da gwmanti da kuma 'yan jarida ,kamar yadda  ofishin jakadancin kasar Amirka da ke kasar ya fidda wata sanarwa in da ya bayyana gamsuwa da wannan ci gaba da kasar ta fara samu na sakin Fursinoni.

Sauti da bidiyo akan labarin