An sako dan takarar shugabancin kasa a Tunisiya | Labarai | DW | 09.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sako dan takarar shugabancin kasa a Tunisiya

Kotu a Tunusiya ta amince a saki dan takarar shugabancin kasar da aka yi a watan jiya, Nabil Karoui da ake tsare da shi. Nabil Karoui ne ya zo na biyu a zagayen farko na zaben. 

Umurnin kotun na zuwa ne gabanin zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar a ranar Lahadi mai zuwa 13 ga wannan wata na Oktoba. 

Mahukuntan kasar ta Tunusiya sun kame Karoui a watan Agustan wannan shekara da muke ciki, bayan tuhumarsa da rashin biyan kudin haraji da kuma musayar kudi ba bisa ka'aida ba. 

Nabil Karoui mai shekaru 56 a duniya ya yi fice wajen sukar lamirin gwamnatin kasar ta wani gidan talabijin mai zaman kansa da ke zama mallakinsa.