An saki Oscar Pistorius daga gidan yari | Labarai | DW | 20.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki Oscar Pistorius daga gidan yari

Hukumomi a Afirka ta Kudu sun sallami dan tseren nakasassun nan Oscar Pistorius daga gidan yari shekara guda bayan da aka daure shi sakamakon kisan budurwarsa.

Cikin daren jiya Litinin ce aka fidda Pistorious din daga gidan kaso kana aka kai shi gidan kawunsa inda zai shafe sauran shekarun da suka rage masa karkashin daurin talala.

Tuni dai 'yan uwan Oscar Pistorious din suka tabbatar da isarsa gida kuma nan gaba a yau ne suka ce za su yi jawabi ga manema labarai kan wannan batu.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne aka yankewa Pistorious din hukunci bayan da kotu ta same shi da laifi na kisan budurwasa Reeva Steenkamp ba da niyya ba lokacin da ya yi zargin cewar wani ya yi masa kutse cikin gidansa.