An sake yin girgizar kasa a Indonesiya | Labarai | DW | 14.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake yin girgizar kasa a Indonesiya

An saba samun iftila'i na girgizar kasa a Indonesiya da ke nahiyar Asiya. Na wannan karon da ya faru a gabashin kasar ya kai karfin maki 7.3 a ma'aunin Richter. Sai dai ba a bayyana asarar da ta haddasa ba tukuna.

Wata mummunar girgizar kasa mai karfi maki 7.3 a ma'unin Richter ta afku a tsibirin Halmahera da ke gabashin Indonesia. Hukumomin kasar ba suka kai ga bayyana barnar rayuka ko dukiyoyi da iftila'in ya haifar ba. Amma an fuskanci katsewar wutar lantarki a wasu sassa na kasar sakamakon iftila'in, ko da yake hukumomin sun nunar da cewa an yi nasarar dawo da ita.

kasar Indonesiya ta saba fuskantar girgizar kasa da matsalar igiyar ruwan Tsunami. Ko da a shekarar da ta gabtaa, sai da wata girgizar kasa mai karfin maki 7.5 a ma'aunin Richter da kuma igiyar ruwan tsunami suka afku a  tsibirin Celebes tare da lamshe rayukan mutane fiye da dubu biyu da 200.