1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake kubutar da matasa daga kogo aThailand

Yusuf Bala Nayaya
July 9, 2018

An sake samun dama ta fito da yaran nan da suka makale cikin kogo sanadin ambaliyar ruwa a arewacin Thailand kamar yadda kwararrun kasa da kasa wajen iya linkaya suka bayyana.

https://p.dw.com/p/316bX
Thailand Höhle | Rettungsaktion Jugendliche
Hoto: Getty Images/L. Phan

Wannan dai ya sanya adadin wadanda aka ceto a aikin gwanayen iya linkayar cikin kwanaki biyu suka kai su takwas. A cewar Narongsak Osottanakorn kwamandan masu aikin bincike da kokarin ceto matasan, da yake jawabi ga manema labarai an garzaya da matasan hudu zuwa asibiti.

Ya kara da cewa labari me dadi a aikin na wannan rana shi ne aikin da suka yi ya daukesu sa'oi tara, sa'oi biyu kasa da aikin da aka yi na farko a ranar Lahadi, matakin da suke ganin zai taimaka wajen tseratar da rayuwar baki dayan matasan da ke buga kwallo su 12 da mai horas da su. A ranar Talata ce dai za a kammala aikin ceton matasan da suka makale cikin kogon a arewacin Thailand.