1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake cafke Kabiru Sokoto

February 10, 2012

Jami'an leƙen asiri a Najeriya sun kuma cafke Kabiru Sokoto jami'in Boko Haram wanda ya tsere.

https://p.dw.com/p/141Zt
This image released by Saharareporters shows police and rescue workers after a large explosion struck the United Nations' main office in Nigeria's capital Abuja Friday Aug. 26, 2011, flattening one wing of the building and killing several people. A U.N. official in Geneva called it a bomb attack. The building, located in the same neighborhood as the U.S. embassy and other diplomatic posts in Abuja, had a huge hole punched in it. (Foto:Saharareporters/AP/dapd)
Hoto: dapd

Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce sun sake cafke Kabiru Sokoto mutumin da ake zargi da kasancewa kan gaba wajen kai mummunan harin Bam na ranar Kirsimeti a garin Madalla wanda ya kuɓuce a hannun 'yan sanda ya tsere a watan da ya gabata. 'Yan sandan sun ce sun yi nasarar sake cafke Kabiru Sokoto ne yau Juma'a a wata 'yar Bukka a garin Mutum biyu a gabashin jihar Taraba da ke kan iyaka da ƙasar Chadi. Hukumar leƙen asiri ta SSS ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa a yanzu haka an tafi da Kabiru Sokoton zuwa Abuja. A ranar 18 ga watan janairun da ya gabata ne Kabiru Sokoto ya tsere daga hannun 'yan sanda a wani yanayi da hukumomin tsaro suka baiyana da cewa mai ɗaure kai, lamarin kuma da ya kai ga shugaban ƙasar Goodluck Jonathan ya kori sufeton 'yan sandan ƙasar Hafizu Ringim da mataimakansa su shida. Ƙungiyar Boko Haram ta ayyana ɗaukar alhakin kai harin na Chochin St Theresa a garin Madalla dake kusa da Abuja.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

.