An sace wani Bajamushe a Gombi ta Adamawa | Labarai | DW | 16.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace wani Bajamushe a Gombi ta Adamawa

Ba a san wadanda suke sace Bajamushen ba. Amma dai a karamar hukumar Gombi da ke Jihar Adawama ta Najeriya ce al'amarin ya auku.

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi awun gaba da wani Bajamushe da ke aiki da cibiyar koyon sana'ar hannu (TTC) da ke karamar hukumar Gombi a Jihar Adamawa ta Tarayyar Najeriya. Da misalin Karfe bakwai na safiyar wannan Larabar ce wannan al' amari ya auku a anguwar Nitel. Maharan sun yi kwantar bauna lullube da borgo a fuskarsu, suka sace wannan Bajamushen cikin motarsa, tare da daure shi kan babur domin yin awun gaba da shi.

'Yan bangan wannan yanki na Gombi sun bi sawun wadannan mutane. Amma rahotanni da ke zuwa yanzu daga Yola na tabbatar da cewa an kashe ‘yan banga biyu da suka bi mutanen. Tuni ma aka rigaya aka dawo da gawarwakinsu. Karamar hukumar Gombi na zaman dar-dar a yanzu haka sakamakon wannan ta'asa.

Mawallafi: Abdulraheem Hassan daga Yola
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe