1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun halaka mutane a Zamfara

June 4, 2023

Harin na daga cikin hare-hare mafi muni da suka faru, tun bayan da aka rantsar da sabon gwamna Dr. Dauda Lawan a wannan jiha da ke da tarihin rashin tsaro a Najeriya.

https://p.dw.com/p/4SAvZ
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare Hoto: Dauda Lawal/Facebook

Wasu 'yan bindiga sun sace mata kusan 30 bayan kashe mutane 26 a yankunan karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne lokacin da maharan suka kai wa al'ummar yankunan hari, inda aka yi dauki-ba-dadi da su.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara SP Shehu Muhammad bai amsa wayar da DW da ta tuntube domin ya yi karin haske kan lamarin ba.

Jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya itama ta bayar da rahoton cewa wasu 'yan bindiga sun kai wani mummunan hari irin na jihar Zamfara, a makwabciya- jihar Sokoto, inda a a yankin Tangaza suka halaka mutane 37.