An sace mata 60 a arewacin Najeriya | Labarai | DW | 24.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace mata 60 a arewacin Najeriya

Mata da haɗe da 'yan mata sitin ake kyautata zaton cewar 'yan Ƙungiyar Boko Haram sun sace a Kummabza da ke cikin jihar Borno.

Kafofin watsa labarai a Najeriya sun ba da labarin cewar wasu mutanen waɗanda ake kyautata zaton cewar yan Ƙungiyar Boko Haram ne suka yi awan gaba da matan. Jaridar Daily Trust ta ce 'yan matan da aka sacen suna da shekaru uku zuwa 12, a ƙauyen da ke kusa da garin Chibok.

Inda a cikin watan Afrilun da ya gabata ƙungiyar ta sace 'yan mata 'yan makarana sama da 200. Majiyoyin sun ce lamarin ya auku ne a cikin jerin hare-haren da suka faru a makon jiya amma sai a wannan makon aka bayyana labarin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo