An sace ma′aikatan Red Cross a Afghanistan | Labarai | DW | 16.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace ma'aikatan Red Cross a Afghanistan

An ba da rahoton cewar wasu 'yan bindigar sun sace wasu ma'aikatan ƙuingiyar su guda biyar a garin Herat da ke a gabashin ƙasar.

Ƙungiyar ta Red Cross ta ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a sa'ilin da tawagar ma'aikatan ke kan hanyarta ta zuwa garin Herat a cikin mota.

A jiya jumma'a ma kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun rawaito cewar 'yan Taliban sun sace wasu jami'an masu aikin cire nakiyoyi a garin Ghazni da ke a yankin yammaci. Hukumomin tsaro na ƙasar ta Afghanistan sun gargaɗi baƙi da su riƙa sanar da su tafiye-tafiyensu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zeinab Mohammed Abubakar