Za a rantsar da gwamnatin wucin gadin Bangladesh
August 7, 2024Jagoran da ke shirin karbar ragamar gwamnatin rikon kwarya a Bangladesh, masanin tattalin arziki Muhammad Yunus ya bukaci al'ummar kasar su kwantar a hankulansu, tare da bukatarsu da yin amfani da wannan dama wajen bunkasa kasar.
Yunus zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar Bangladesh, biyo byan ajiye mukami da tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina ta yi sakamakon zanga-zangar makonni da al'umma suka yi.
Shi dai Yunus mai shekaru 84 a duniya sabon jagoran gwamnatin rikon kwaryar, ya jaddada bukatar kwantar da hankula ga al'ummar kasar, maimakon tayar da tarzoma. Yunus dai na cikin jagororin adawar da gwamnatin Hasina ta rinka musgunawa, kafin dalibai su tursasa mata ta ajiye mukaminta ta hanyar zanga-zanga. Gobe Alhamis ake sa ran rantsar da sabuwar gwamnatin wucin gadin ta Bangladesh kamar yadda rundunar sojan kasar ta nunar.