An rattaba hannu kan shirin zaman lafiya a Mozambik | Labarai | DW | 05.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rattaba hannu kan shirin zaman lafiya a Mozambik

'Yan tawaye da shugaban kasar Mozambik sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da nufin kawo karshen rikicin kasar.

A birnin Maputo na kasar Mozambik shugaban kasa Armando Guebuza da jagoran 'yan adawa Afonso Dhlakama sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya, wanda hakan ya kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru biyu ana yi. A shekarar 2012 kungiyar 'yan tawaye ta Renamo ta kaddamar da fada a kan jam'iyyar da ke mulki ta Frelimo, wadda ke mulki a kasar tun a 1975. Kafin sabon fadan dai kungiyoyin biyu sun kwashe kusan shekaru 20 suna gwabza kazamin yakin basasa. Sabuwar yarjejeniyar ta tanadi shigar da mayakan Renamo cikin rundunar sojin kasar sannan 'yan adawa za su samu karin wakilci wajen sanya ido a zaben kasar. Mozambik na a jerin kasashe mafi karancin ci gaba a duniya duk da dimbin ma'adanan karkashin kasa musamman kwal da iskar gas da take da su.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman