An rantsar da shugaban ƙasar Mali | Labarai | DW | 04.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da shugaban ƙasar Mali

Ibrahim Boubacar ya sha rantsuwar kama aiki, a wani ƙwarya-ƙwarya bikin da aka gudanar kafin a yi wani ƙasaitaccen bikin a nan gaba.

A lokacin da ya ke yin rantsuwar shugaban ya sha alwashin kare jamhuriya tare mutunta kudin tsarin mulki da kuma sa a yi aiki da shi. An dai zaɓi IBK ne mai shekaru 68 da haifuwa a cikin watan jiya a wani wa'adin mulki na shekaru biyar.

Tun da farko dai, sai da ka yi ban hannu na mulkin a safiyar yau tsakanin sabon shugaban da kuma shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya Dioncouda Traore. Babban ƙalubalen da ke a gaban shugaban shi ne na sake haɗa kawunan al'ummar ƙasar bayan yaƙin da ƙasar ta yi fama shi. Nan gaba ne ai a rana 19 ga wannan wata za gudanar da wani ƙasaitaccen bikin rantsar da shugaban a gaban shugabannin ƙasashen duniya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Saleh Umar Saleh