An rantsar da sabon shugaban Tunisiya | Labarai | DW | 31.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da sabon shugaban Tunisiya

A wannan Laraba ce Béji Caid Elssebsi, da ke a matsayin zababben shugaban kasar na dimokradiyya a tarihinta ya yi rantsuwar kama mulkin Tunisiya.

A cikin wani takaitaccan jawabi da ya yi, bayan da aka rantsar da shi, sabon shugaban kasar ya yi alkawarin zama shugaban dukkan 'yan kasar Tunisiya, inda ya yi kira ga sasantawa tsakanin jam'iyyun siyasar kasar da ma kungiyoyin fararen hula. Shugaba Caid Elssebsi ya kara da cewa, babu wani ci gaban kasar Tunisiya a nan gaba, idan babu hadin kan al'ummar kasar, yayin da mutane da dama ke nuna shakkunsu kan kasancewar tsofin membobin gwamnatin tsohon shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali a kusa da shi.

A ranar 21 ga watan nan na Disamba ne dai aka zabi sabon shugaban kasar ta Tunisiya wanda ya samu kashi 55 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, gaba da abokin hamayyar shugaban mai marin gado Moncef Marzouki.