An rantsar da sabon firaministan kasar Ostareliya
September 15, 2015Talla
A wannan Talata an rantsar da Malcolm Turnbull hamshakin mai-arziki kana tsohon ma'aikacin banki a matsayin sabon firaministan kasar Ostareliya, wanda ya yi alkawarin samar da aiki da bunkasa tatttalin arzikin kasar. Turnbull ya maye gurbin Firaminista Tony Abbott bayan ya samu nasarar zaben shugabancin jam'iyya mai mulki, inda ya zama mutum na hudu da ya rike mukamun cikin shekaru biyu da suka gabata.
Sabon Firamnista Malcolm Turnbull na kasar ta Ostareliya dan shekaru 60 da haihuwa ya taba rike mukamun ministan sadarwa.