An rantsar da saban shugaban ƙasar Nigeria | Labarai | DW | 29.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da saban shugaban ƙasar Nigeria

A Tarraya Nigeria an rantsar da saban shugaban ƙasa El-Haji Umaru Musa yar Aduwa, wanda yau a hukunce, ya gaji tsofan shugaban Olesegun Obasanjo.

Idandai ba amanta ba, hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria, ta bayyana Yar Aduwa, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 21 ga watan Aprul, tare da ƙuri´u kussan milion 25, a yayin da mai bi masa,wato Jannar Muhamadu Buhari mai ritaya, ya samu ƙuri´u milion kussan 7.

Bayan shugaban ƙasar kotin ƙoli ta rantsar da mataimakin sa, Goodluck Jonathan, tsofan gwamna jihar Bayelsa.

Sannan a jihohi daban-daban, an rantsar da sabin gwamnoni.

A lokacin bikin rantsuwar, Umaru Musa Yar Aduwa,mai shekaru 55 a dunia, ya rantse da Alƙur´ani mai tsarki , tare alƙawarta gudanar da aiki daidai yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.