1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nuna goyon bayan haramta hukuncin kisa

November 16, 2007
https://p.dw.com/p/CHux
Tare da gagarumin rinjaye MƊD ta nuna goyon bayan ta ga daina aiwatar da hukuncin kisa a duniya baki ɗaya da nufin haramta yanke hukuncin kisa. A ƙuri´ar da ta kaɗa ƙasashe 99 na hukumar kare hakkin bil Adama ta majalisar sun goyi da bayan wannan mataki yayin 52 suka ki sannan ƙasashe 33 suka yi rowan ƙuri´unsu. Tarayyar Jamus da kuma sauran ƙasashen KTT, EU na daga cikin kasashen dake goyon bayan matakin na haramta hukuncin kisa. Alkalumman ƙungiyar kare hakin bil Adama ta kasa da kasa wato Amnesty International sun yi nuni da cewa har yanzu ƙasashe 66 na aiwatar da hukuncin kisa.