An nuna goyon baya ga gamaiyar ′yan adawar Siriya | Siyasa | DW | 12.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An nuna goyon baya ga gamaiyar 'yan adawar Siriya

Ƙasashen duniya dake kiran kansu "ƙawayen Siriya" sun yi maraba da girka gamaiyar 'yan adawar Siriya da za ta jagoranci hambarar da shugaba Bashar alAssad.

Wasu wasu daga cikin ƙasashen sun fara amincewa da gamaiyar a matsayin halattatciyar hukuma ɗaya tilo ta al'ummar ƙasar ta Siriya.

Bayan fiye da mako ɗaya ana kai ruwa rana a birnin Doha na ƙasar Qatar, daga ƙarshe yan adawar na Siriya sun dunƙule ƙarkashin jagorancin Ahmad Hamza Elkhatib, wani mai wa'azin Islama dake da matsakaicin ra'ayi, wanda ya bar ƙasar ta Siriya watanni uku da suka gabata. kana aka zaɓa masa mataimaka biyu, wani hanshakin ɗan kasuwa, Riyadh Assaif da kuma wata mace mai fafutuka, Suhair Altasi.

Goyon baya ga haɗakar 'yan adawar Siriya

Tuni dai ƙasashen da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen shirya taron da ya kai ga kafa gamaiyar suka nuna cikakken goyan bayansu ga haɗaɗɗiyar ƙungiyar har ma ƙasar Faransa ta ce, ta amince da halaccin gamaiyar a hukumance. Ƙamar yadda wasu ƙasashen da aka saye sunayensu suka yi alƙawarin ba wa 'yan tawayen makamai, a ta bakin mataimakin shugaban gamaiyar Riyadh Assaif.


"An mana ƙwaƙƙaran alkawarin taimaka wa 'yan tawaye damar kare kansu da ma fararen hula, ta hanyar ba su makaman da za su iya harbo jiragen yaƙi, da zai iya tarwatsa motoci masu sulke."

Ƙasar Amirka da a makwannin da suka gabata ta nemi da a kafa sabuwar gamaiyar 'yan adawar, a ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta ta yi alƙawarin ƙara tallafin da take ba wa 'yan tawayen, da kuma fara tattauna yiwuwar amincewa da su a matsayin wakilan gwamnatin Siriya a hukumance.

Shi kuwa ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague bayan da ya taya 'yan tawayen murnar haɗewar da suka yi, ya ce ƙasarsa za ta gaiyaci taron ƙawayen Siriya ranar Juma'a mai zuwa, don yi wa 'yan tawayen gidauniyar kuɗi.

Babu ja da baya wajen tallafa wa 'yan tawaye

A nasa ɓangaren, ministan harkokin wajen Turkiya cewa ya yi, a yanzu kam ƙasashen duniya ba su da wani hanzari na jan ƙafa wajen tallafa wa 'yan tawayen da duk abin da ya dace don al'ummar ƙasar Siriya su cimma burinsa na samun sauyi.

A ta ɓangarsen ƙasashen Larabawa kuwa, a yanzu haka, ƙungiyar Larabawa dake Alƙahira, tana nan tana tattaunawa kan amincewa da gamaiyar 'yan tawayen a matsayin halattattun jagororin Siriya, lamarin da kadan har ya tabbata, zai ba wa 'yan tawayen damar ƙwace ofisoshin jakadancin dake ƙasashen Larabawan daga jami'an gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin