An nemi tsaida kirga kuri′u a Bangui | Labarai | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi tsaida kirga kuri'u a Bangui

Kusan ashirin cikin talatin na wadanda suka tsaya takarar shugabancin wannan kasa na sukar aikin kidaya kuri'un.

Afrika Wahlen in Zentralafrika

Masu kada kuri'a a Bangui

An bukaci mahukunta a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya su tsaida duk wani aiki na kirga kuri'un zaben da aka kada dan zaben shugaban kasa da aka yi a makon da ya gabata saboda abin da suka kira gano aringizon kuri'un zabe a aikin kirga kuri'un. Kusan kashi ashirin cikin talatin na wadanda suka tsaya takarar shugabancin wannan kasa a ranar Litinin din nan sun bayyana wa taron manema labarai cewa akwai magudi a zaben.

Wannan kalubalanta dai ta 'yan takarar ga wannan aikin kidaya kuri'u na zama wani koma baya da hukumar da ta tsara zaben ta gamu da shi, ganin yadda ta sa himma cike da fatan zaben da ta shirya a ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata zai zama sanadi na samun kwanciyar hankali a kasar me fama da tashin hankali mai nasaba da rikicin addini da kabilanci da ya yi sanadin mutane dubbai wasu kuma sama da miliyan daya suka kaurace wa muhallansu a tsawon shekaru uku da kasar ta yi na tashin hankali.