1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An nemi taimakon Amirka a magance rikicin kasar Habasha

Ramatu Garba Baba
February 3, 2021

Tsoffin jakadun Amirka da wasu tsoffin jami'an da suka yi aikin wanzar da zaman lafiya ne suka nemi sabuwar gwamnatin Amirka da ta saka baki a shawo kan rikicin kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/3oqJ3
Äthiopien I  Sudan I Konflik
Hoto: Ashraf Shazly/AFP

Mutanen da suka zarta 300, suna son Amirka ta samar da maslaha ta hanyar samun zaman lafiya da damar isar da kayayyakin agaji ga mabukata, baya ga haka suna son a gudanar da binciken laifuka na yaki da aka aikata a tsawon lokacin da aka kwashe ana gwabza fada a tsakanin sojin gwamnati da mayakan TLP. A takardar da suka turawa majalisar Amirkan, sun baiyana damuwa kan halin da rayuwar fararen hula sama da miliyan shida ke ciki a yankin na Tigray da rikici ya daidaita.

An dai shiga wata na hudu da barkewar rikici a kasar da ta fi yawan al'umma a yankin kahon Afirka, baya ga asarar rayuka da dukiya, akwai zarge-zarge na cin zarafin mata da yara kanana da kuma hana masu aikin agaji shiga yankin don taimaka wa jama'ar da ke cikin tsanani na bukatar taimako. Gwamnatin Habashan ta musanta wadannan zarge-zargen inda ta zargi bangaren Tigray da zuzuta munin rikicin a idon duniya.