An nemi Japan ta dakatar da wata tashar nukliyarta | Labarai | DW | 19.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi Japan ta dakatar da wata tashar nukliyarta

Kungiyar kare muhalli ta kasa da kasa ta bukaci Japan ta dakatar da aikin tashar nukliyar ta Sakurajima da ke fuskantar barazanar wani dutsi mai aman wuta.

A kasar Japan kungiyar kare muhalli ta kasa da kasa ta Greenpeace ta yi kira ga hukumomin kasar da su dakatar da aikin wata tashar nukliya da ke a yankin tsauni Sakurajima na Kudu maso Yammacin kasar wanda ya fara aman wuta a cikin daran Talata washe garin wannan Laraba. Dama dai tun ranar 15 ga wannan wata na Ogusta ne hukumomin karamar hukumar Kagoshima inda dutsin mai aman wutar ya ke suka gargadi jama'ar da ke kusa da dutsin mai tsawon kilomita 1.117 da su kaura, ganin irin yanda ake kara samun alamun zai fara aman wutar tasa.

Tashar nukliyar da kungiyar ta Greenpeace ta bukaci kasar Japan din ta dakatar da aikinta na a nisan kilomita 50 kawai da dutsin mai aman wutar na Sakurajima. Dama yau da kwanaki hudu kenan da hukumomin kasar ta Japan suka tayar da wannan tashar nukliya wacce ta ke daya daga cikin tashohin nukliya 48 na kasar ta Japan da aka tsaida aikinsu tun bayan abkuwar hadarin Fukushima