1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Nadin sabbin ministocin gwamnati

Abdullahi Tanko Bala
June 11, 2021

Kasar Mali ta sanar da kafa sabuwar majalisar gudanarwar gwamnati inda sojoji ke rike da manyan mukamai a cikinta a cewar wata sanarwa da kafar yada labaran kasar ta  baiyana.

https://p.dw.com/p/3umYJ
Mali Oberst Assimi Goita, Anführer der malischen Militärjunta
Hoto: Francis Kokoroko/File Photo/Reuters

A ranar larabar da ta gabata ce dai aka rantsar da Kanar Assimi Goita wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a watan da ya wuce a matsayin shugaban kasa inda kuma shugaban ya nada Firaminista farar hula.

A baya ma dai Goita shi ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da zababben shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita bayan tsawon makonni ana zanga zanga kan cin hanci da ya yi wa gwamnatin katutu da rikicin masu gwagwarmayar jihadi.

A sabuwar majalisar ministocin da aka nada sojojin sun dawo da kanar Sadio Camara a matsayin ministan tsaro bayan cire shi da aka yi a baya wanda yana daya daga cikin dalilan da suka janyo kifar da gwamnatin shugaba Bah Ndaw a watan da ya gabata.

Ana dai ganin mai yiwuwa kafa sabuwar gwamnatin ya sassauta damuwar da aminan Mali da shugabannin yankin suke nunawa wadanda ke bukatar gwamnatin rikon kwaryar ta fara shirin mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya.