An nada sabon firaminista a kasar Tunisiya. | Labarai | DW | 05.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabon firaminista a kasar Tunisiya.

Habib Essid ne sabon firaministan kasar Tunisiya. Tuni ya fara shirye shiryen kafa sabuwar gwamnatinsa.

Sabon firaministan mai shekaru 65 da haihuwa kuma tsofon ministan cikin gidan kasar, ya rike mukammai da dama a lokacin mulkin tsofon shugaban kasar Ben Ali. Da yake magana ga manema labarai, sabon ya abun da ya rage shi ne na shiga tattaunawa da bangarorin siyasar kasar da ma na kungiyoyin fararen hulla, don samun fitar da sunayan membobin sabuwar gwamnati.

Jam'iyyar da ta yi nasara a zaben 'yan majalisun Tunisiya ta Nidaa Tounès ce ta gabatar da sunansa a matsayin wanda ta ke so a dora wa wannan nauyi. A cewar mataimakin shugaban wannan jam'iyya kuma shugaban majalisar dokokin kasar Mohamed Ennaceur, zaben Habib Essid na da mahimmancin gaske, ganin yadda yake a matsayin mutun na tsakiya. Sannan yana da sani kan harkokin tsaron kasar.