1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin lamba ya janyo nadin gwamnati a Mali

September 21, 2020

Kanal Bah Ndaw mai ritaya shi ne sabon jagoran gwamnatin rikon kwarya, wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin tsaro, kana Kanal Assimi Goita zai taimaka masa,

https://p.dw.com/p/3ioK2
Militärjunta in Mali ernennt Übergangs- und Vizepräsidenten
Hoto: ORTM TV/dpa/picture-alliance

Biyo bayan matsin lamba daga kasashe makwabta da kungiyar habbaka tattalin arzikin yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEO, sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Mali sun bayar da sanarwar kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Dama can shugabannin kasashen yammacin Afrika sun jajirce lallai sai an kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula da zata sake maida madafun iko ga hannun wata zababbar gwamnati cikin watanni 18, ko da kuwa mataimaki zai kasance daga bangaren 'yan juyin mulkin inda Kanal Assimi Goita ya kasnce mai taimakawa sabuwar gwamnatin.