An naɗa sabon firaminista a Mali
December 12, 2012Wani ƙudirin gwamnatin da gidan telbijan na ƙasar ta Mali ya baiyana wato ORTM ,ya sanar da cewar shugaban gwamnatin wucin gadi Dioncounda Traoré, ya naɗa Diango Cissoko a matsayin sabon firaministan.
Cissoko ɗan shekaru 62 da haifuwa shi ne ke riƙe da muƙamin mai sasantawa na ƙasar tun a cikin watan Mayo na shekara bara.
Da ya ke magana da manema labarai Diango Cissokon ya ce abu na farko da ke a gaban sa shi ne shirya zaɓe;da sake ƙwato yankin arewacin ƙasar daga cikin hanu yan'tawayen sannan kuma ya ce zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.Kuma ya ƙara da cewar.Ya ce ''tare gaba ɗaya cikin haɗin kai zamu iya fuskantar man'yan ƙalubalan da ke a gaban mu ga ƙasar da ta rabu gida biyu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas