An kwashe mata da kananan yara daga Yola | Labarai | DW | 21.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwashe mata da kananan yara daga Yola

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta tabbatar da kwashe wasu mata da kananan yara akalla 275 daga sansanin gudun hijira da su ke ciki a Yola.

Jami'in hukumar na jihar Adamawa Malam Saad Bello, ya ce ofishin mai bada shawara kan harkokin tsaron kasa ne ya kwashe mata da yaran a jiya Laraba, sai dai shi ma jami'in bai san takamaiman wajen da aka kai su ba a halin yanzu.

Rashin sanin wajen da mutanen su ke dai na ci gaba da zama abin muhawara a jihar ta Adamawa, wadda ko a bayan-bayan nan ma ta fuskanci harin kunar bakin wake a kasuwar garin Garkida dake arewacin jihar, harin da aka dora alhakinsa a kan 'yan Boko Haram.