An kwantar Nelson Mandela a asibiti | Labarai | DW | 08.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwantar Nelson Mandela a asibiti

Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela ya yi fuce gurin karfafa Demokradiya a kasarsa da ma Nahiyar Afrika baki daya.

Rahotani daga birnin Johanesburg na Afrika ta Kudu,sun tabbatar da cewar an kwantar da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela a wata asibitin Birnin Pretoria bisa binciken lafiyarsa da ke kara tabarbarewa a kowane lokaci sakamakon tsufa. Kodayake jami'an asibitin sun bayana cewar tsohon shugaban dan shekaru 94 da haifuwa na cikin koshin lafiya idan aka yi la'akari da adadin shekarun nasa.
Fadar shugaba Jacob Zuma ce ta bayana labarin kwantarda lattizon a asibiti. Neson Mandela dai shi ne shugaba bakar fata na farko da kasar ta samu tun bayan kawarda mikin wariya da ya dade yana cin zarafin al'ummar masu launin fata baka,abunda ya kaishi gidan wakahi har na tsawo shekaru 27.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Halima Balaraba Abbas