An kwantar da Hillary Clinton a asibiti | Labarai | DW | 31.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwantar da Hillary Clinton a asibiti

Rasin lafiyar da ke damunta ne ta sa Clinton ta kasa amsa kira a gaban komitin dattawan Amirka domin bada bahasi a kan harin da aka kaiwa ofishin jakadancin kasar a Libiya.

default

Hillary Clinton

A wannan Lahadi ne da yamma, aka kwantar da Hillary Clinton a wani asibitin da ke birnin New York na Amirka bayan da ta yanke jiki ta fadi biyo bayan wani ciyon da ya bige ta. Hillary Clinton 'yar shekaru 65 da haifuwa matar tsohon shugaban kasar Amurka, Bill Clinton, ta rike mukamin sakteriyar harakokin wajen Amurka a tsawon wa'adin farko na shugaba Obama wanda ya nada ta. Rahotani dai sun ce tana fama ne da cutar sandarar jini inji mashawarcinta Philippe Reines. Ta dai share kusan makonni biyu ba wanda ya sa ta a ido, tun bayan da ta aje mukamin nata inda a ka maye gurbinta da tsohon dan takarar jam'iyar Demokrat John Kerry wanda ya fafata da shugaba George Walter Bush. To sai dai bisa ga rahotannin da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito, Hillary Clinton na karbar jinya inda ake sa ran za ta bar asibitin nan ba da jimawa ba.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal