An kori ministan wasannin kasar Moroko | Labarai | DW | 07.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori ministan wasannin kasar Moroko

Sarkin Mohamed na shida na kasar Moroko ya sallami ministan wasannin kasar daga bakin aiki sakamkon sakamakon sakaci.

Sarki Mohamed na VI na kasar Moroko ya sallami ministan wasannin kasar Mohammed Ouzzine daga bakin aiki, saboda yadda bincike ya nuna sakacin ma'aikatar lokacin da kasar ta karbi wasannin kungiyoyin duniya a watan da ya gabata na Disamba.

Sarkin ya ce sakaci ma'aikatar wasanni ne lokacin da aka samu matsala a wasan kusa da na karshe a Rabat babban birnin kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe