An kori ministan tsaron Mali daga bakin aiki | Labarai | DW | 04.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori ministan tsaron Mali daga bakin aiki

An kori Tieman Hubert Coulibaly daga mukamun ministan tsaron Mali sakamakon yadda ake samun sabbin hare-hare mayaka masu dauke da makamai.

Rikicin da ke ci gaba da faruwa a kasar Mali ya yi awun gaba da ministan tsaron kasar Tieman Hubert Coulibaly, wanda cikin wata sanarwa ta gwamnati aka bayyana tubeshi daga mukamunsa. Matakin ya zo kwana guda bayan sojojin gwamnati da tallafin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun sake kwato garin Boni da ke tsakiyar kasar da 'yan bindiga suka karbe iko da shi na wani lokaci ranar Jumma'a.

Tuni gwamnati ta bayyana nada Abdoulaye Idrissa Maiga tsohon ministan kula da filaye a matsayin sabon ministan tsaron kasar ta Mali, wanda yake da gagarumin kalubale kawo karshen hare-haren mayakan masu dauke da makamai galibi masu ikirarin jihadi.