An koma tattaunawar hadin kan Libya | Labarai | DW | 11.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma tattaunawar hadin kan Libya

Ana saran wakilan majalisar kasar Libyan shiga batun tattaunawar bayan da suka kaurace wa zaman tatatunawar a makon daya gabata.

Libyen Suheirat Gespräche Parlament UN

Mahalarta taron tattauna rikicin Libya

A ranar Talata ce bangarorin da basa ga miciji da juna a kasar Libya suka fara wata tattaunawar da za ta kai ga samar da gwamnatin hadin kan kasar tare da samun halartar wakilai daga ko wanne bangare.

Ana saran wakilan majalisar kasar Libyan shiga batun tattaunawar bayan da suka kaurace wa zaman tatatunawar a makon daya gabata.

Yanzu haka dai bangarori biyu ne ke kokarin karbar madafun iko a kasar.

Libya dai ta tsunduma cikin rikici ne bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Moammar Ghadaffi a shekara ta 2011.

Bugu da kari wani manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya Bernardino Leon wanda ke shiga tsakanin batun tattaunawar da aka fara a birnin Geneva ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi kokarin cimma yarjejeniyar kafin karshen wannan watan da muke ciki.