An koma da tsohon shugaban Peru Alberto Fujimori gida | Labarai | DW | 22.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma da tsohon shugaban Peru Alberto Fujimori gida

Tsohon shugaban kasar Peru Alberto Fujimori yana kan hanyar sa ta komawa kasar a karkashin tsaron ´yan sanda kwana guda bayan da kotun kolin kasar Chile ta ba da umarnin tasa keyarsa zuwa Peru inda ake zargin sa da laifin keta hakin bil Adama da cin hanci da rashawa. Da misalin karfe daya agogon GMT wani jirgin saman rundunar ´yan sandan Peru ya tashi daga birnin Santiago na kasar Chile zuwa Lima babban birnin Peru dauke da Fujimori mai shekaru 69. Da farko dai an binciki lafiyarsa don tabbatar da ko zai iya yin wannan tafiya zuwa kasar ta Peru.