An koma da Sharon dakin tiyata | Labarai | DW | 05.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma da Sharon dakin tiyata

An mayarda firaministan Israila Ariel Sharon dakin tiyata,sakamakon bugun zuciya da kuma hawan jini da ya samu a daren jiya.

Likitoci suna kokarin janye jini daga kwakwalwar Sharon,bayan bugun zuciya daya samu.

Yanzu haka an mika ragamar mulki hannun mataimakinsa Ehud Olmert.

Likitocin sunce sun samu nasarar dakatar da kwararar jini cikin kwakwalwarsa bayan tiyata na kusan saoi 6,amma an sake mayarda shi dakin tiyata domin ci gaba da tiyatar, wadda darektan asibitin Shlomo Yosef yace zai dauki saoi da dama,yana mai baiyana matsanancin halin da Sharon yake ciki.